1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Boko Haram na cigaba da hare-hare a Borno

Zulaiha Abubakar
February 14, 2019

Mayakan Boko Haram sun kai wa tawagar yakin neman zaben gwamnan jihar Kashim Shettima hari a hanyar Dikwa zuwa Ngala.

https://p.dw.com/p/3DLsI
Nigeria Kashim Shettima, Gouverneur Borno
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Al'umma na bayyana damuwa sakamakon bacewar mutane da dama wadanda ake zaton mayakan Boko haram sun sace, ciki har da masu sarautar gargajiya uku da wani babban sakatare a fadar gwamanan jihar Borno, gami da wasu ‘yan siyasa da matasan aikin tsaro na sa kai. Biyo bayan wani harin kwantan bauna da mayakan Boko Haram suka kai wa tawagar yakin neman zaben gwamnan jihar Bornon. Mummunan harin ya zo ne a kasa da kwanaki biyu a gudanar da zabuka a Najeriya.