1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allurar corona ga masu kula da aikin Hajji

March 26, 2021

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa daga watan gobe zai zama wajibi dukkan ma'aikatan da ke aiki da hukumar kula da aikin Hajji ta kasar su yi rigakafin annobar coronavirus ko su yi gwajin cutar sau daya a duk mako.

https://p.dw.com/p/3rFjm
Saudi-Arabien Mekka | Erste Pilger nach Coronasperrung
Hoto: Saudi Ministry of Hajj and Umra/AFP/Getty Images

Ma'aikatar kula da ayyukan Hajji da Umrah a kasar Saidiyya sun ce sabuwar dokar ta shafi shaguna da kuma wasu karin ma'aikata da ke gudanar da ayyuka na musamman. Dokar rigakafin corona za ta fara aiki ne daga farkon fara azumin watan Ramadan da ake sa ran farawa a ranar 13 ga watan Afrilu, ko da yake har ya zuwa yanzu kasar ba ta fidda adadin wadanda za ta amince su gudanar da aikin Hajjin bana ba.

A farkon wannan watan ne dai ministan lafiyan kasar Saudiyya ya ce allurar rigakafin corona ta wajabta ga dukkan maniyatan aikin Hajjin bana. Tun farkon bullar annobar corona dai, gwamnatin kasar ta dauki matakin dakatar da ayyukan Umrah na dan wani lokacin tare da bai wa tsiraru 'yan kasar damar gudanar da aikin Hajji.