Alkalan Indiya sun soki babban jojin kasar | Labarai | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alkalan Indiya sun soki babban jojin kasar

Alkalai hudu a kotun kolin kasar indiya sun yi hasashen cewar dimukaradiyya na fuskantar barazana saboda yadda ake gudanar da shari’u a kotuna ba tare da bin dokoki ba.

Alkalan sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai irinsa na farko da suka kira inda su ka yi korafi kan babban Jojin kotun koli Dipak mishra cewar baya bin dokokin da aka shimfida a tsarin aikinsu, sannan yana yin yadda ya so da shari'un da aka gabatar masa. Ya zuwa yanzu dai babu wani martanin kare kai daga babban Jojin kotun kolin.

Daga bangaren Gwamnatin kasar kuwa wasu mataimakan Firayim ministan kasar Narendra Modi sun bayyana cewar yana nazarin al'amarin kuma a halin yanzu ya nemi ganawa da Manyan jami'an ma'aikatar Shari'ar kasar don nemo bakin zaren.