1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Nijar: Albasa, sabuwar hanyar samun kudin shiga?

Lawan Boukar LMJ
April 15, 2026

Hukumomin kula da harkokin noma da kiwo da muhalli a Jamhuriyar Nijar, sun kafa wani kwamiti da zai tsara sashen albasa ganin yadda kasar ke sahun gaba wajen noman albasa a yammacin Afrika.

https://p.dw.com/p/5CEQf
Jamhuriyar Nijar | Noma | Albasa
Kokarin inganta noman albasa a Jamhuriyar NijarHoto: Esayas Gelaw/DW

Ana jiran wannan kwamitin ya samar da cikakken tsari, yadda Jamhuriyar ta Nijar da manoman albasar da masu safararta za su ci moriyarta. Nauyin da aka dora wa wannan kwamiti shi ne na narazi da duba dukkanin hanyoyin da suka kamata da sauran dabaru da nan gaba za a yi amfani da su, domin inganta harkokin albasa a Nijar.

Inganci, ko kwarewa?

Hakan kuma na daga cikin tsarin hukumomin Nijar na bunkasa duk wata hanya ta samar da abinci mai yawa da inganci. Wannan fanni na albasa na sahun gaba, idan aka yi la'akkari da yadda albasar Nijar din ke da inganci, kuma kasar ce sahun gaba a fannin noman albasa a kasashen yammacin Afrika.

Manoma sun sauke farashin abinci a Damagaram

Ga masu noman albasa wadanda tun tashinsu abun da suka gada kenan kamar Rilwanou Ibrahim da aka fi sani da Mai ya ce, lalle a yanzu sun lura gwamnati na son bunkasa noma ganin tasiri wajen takin zamani. Sai dai kuma ya ce, dole sai gwamnati ta kara tashi tsaye sosai in har ana so a cimma gacci. Tun dai da jimawa kiran da shugaban kungiyar manoma da makiyaya ta kasa Djibo Bangna ke yi  shi ne a zamanantar da noma da kiwo, idan har ana fatan samun yadda ake so.

Za a cimma nasara?

A cewarsa albasa ba yau ya kamata a ce an dauki matakan da suka dace, domin inganta nomanta ba. Jamhuriyar Nijar dai ita ce kan gaba wajen fitar da albasa a yammacin Afirka, inda ake noma sama da ton miliyan daya a kowace shekara. Sai dai rashin zamanantar da tsarin ta hanyar samar da injina, na hana rawar gaban hantsi a game da noman na Albasa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani