Al-Zakzaky ya zargi sojoji da kashe ′ya′yansa | Labarai | DW | 26.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Zakzaky ya zargi sojoji da kashe 'ya'yansa

Shugaban 'yan Shi'a a Najeriya, ya yi wannan zargi ne bayan da 'ya'yansa uku da magoya bayansa 30 suka rasa rayukansu bayan kammala muzahara a Zaria.

Shugaban 'yan Shii'a a Najeriya Cheikh Ibrahim Al-Zakzaky a wannan asabar din, ya zargi sojojin kasar, da laifin kashe uku daga cikin yayan sa, tare da wasu magoya bayan sa a kalla guda talatin, yayin da suka fito domin zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Gaza ta Falasdinu da ke fuskantar lugudan wuta daga Isra'ila.

Sai dai daga nasu bangare Sojojin da suka yi wannan aiki, sun ce ya zame musu dole ne su maida martani, dangane da harbe-harbe da suka yi ta fito musu daga gungun jama'ar, inda suka ce mutane tara ne suka rasu. Birnin Zaria da ke arewacin Najeriya, ya kasance nan ne cibiyar kungiyar ta 'yan shi'a a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar