Al-Bashir ya sake tsallake tarkon ICC | Labarai | DW | 15.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Bashir ya sake tsallake tarkon ICC

Jirgin Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya tashi daga Afirka ta Kudu a kan hanyarsa ta komawa gida duk kuwa da umurnin dakatar da shi da wata kotu a kasar ta bayar.

Jirgin Al-Bashir ya bar Afirka ta Kudu zuwa Sudan

Jirgin Al-Bashir ya bar Afirka ta Kudu zuwa Sudan

Babbar kotun Afirka ta Kudu ce dai ta bayar da umurnin dakatar da al-Bashir bayan da ta ce ta samu takardar sammacinsa daga kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata laifukan yaki, a yayin da yake halartar taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka AU a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudun. Ita dai kotun ta ICC na tuhumar Shugaba Bashir na Sudan da laifin kisan kiyashi da kuma aikata laifukan yaki a yayin rikicin yankin Darfur na Sudan din. Ana sa ran da zarar Bashir ya isa gida Sudan zai gudanar da taron manema labarai.