Akalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu cikin fada a Afghanistan | Labarai | DW | 19.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu cikin fada a Afghanistan

Jamian kasar Afghanistan sunce mutane akalla 100 wadanda suka hada da farar hula da yan sanda da kuma yan gani kashe ni suka rasa rayukansu cikin kwanaki uku na bata kashi tsakanin dakarun NATO da yan Taliban a kudancin kasar ta Afghanistan.

Tashe tashen hankula a yankin sun haddasa mutuwar fararen hula da dama wanda ya janyo suka da raguwar goyon baya ga dakarun NATO da gwamnatin Hamid Karzai.

A lardin Uruzgan yan sanda sunce yan kungiyar Taliban sun kaddamar da wani hari da ake gani shine mafi girma cikin wannan shekara inda suka kwace wani yanki kusa da Kandahar.