AI ta ce hukuncin kisa ya ragu a duniya | Zamantakewa | DW | 11.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

AI ta ce hukuncin kisa ya ragu a duniya

Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahotonta na shekara-shekara kan batun hukuncin kisa a Duniya, inda alkaluma suka nunar cewar a shekarar 2016 an samu ja baya dangane da aiwatar da hukuncin kisa a duniya.

Rahoton na kungiyar da ke kare hakin bil Adama ta Amnesty International ya ce adadin mutanen da aka zartas da hukuncinn kisa a kansu a duniya ya kai mutun 1.032 a shekarar da ta gabata ta 2016. Alhali a shekara ta 2015 an zartas da hukuncin kisa kan mutane 1.634 a duniya wanda a wannan lokaci adadin ya kasance mafi muni tun daga shekara ta 1989.

Sai dai kuma wannan adadi bai kumshi yawan mutanen da aka zartas wa da hukuncin kisa a kasar China ba, wanda a cewar kungiyar adadin na China shi kadai ya zarta na sauran kasashen duniya amma kuma hukumomin kasar na boye kayansu cikin sirri.

A kasashen Afirka na kudu da Sahara ma duk da cewa an samu ja baya wajen zartas da hukuncin kisan, amma kuma yawan wadanda aka yanke wa hukuncinn kisa ya rubunya na shekara ta 2015, wanda hakan ya dauko tushe ne daga matakin da Najeriya ta dauka wajen yanke hukuncin kisa.  Isa Sanusi babban jami'in hulda da jama'a a kungiyar Amnesty International reshen Tarayyar Najeriya ya tabbatar da wannan matsayi.

Philippinen Unterhaus beschließt Rückkehr zur Todesstrafe | Protest (Reuters/R. Ranoco)

'Yan Philippines ma na adawa da hukuncin kisa

  Baya ma dai ga mataki na Tarayya, su ma jihohi da dama sun yanke hukuncin kisa a kan mutanen da ake tuhuma da manyan laifuka kaman satar mutane dan karbar kudaden fansa da dai sauransu a Najeriya. Sai dai babban Jami'in hulda da jama'a na kungiyar ta Amnesty International reshen tarayyar ta Najeriya Isa Sanusi ya ce akwai jihohin da suka yi fuce a Tarayyar ta Najeriya:

Wannan rahoto na kungiyar ta Amnesty International ya  yi nuni da dan yatsa ga kasar Kamaru wadda tun watanni take fama da tashe-tashen hankula kama daga matsalar 'yan Boko Haram da kuma na al'ummar kasarta da ke magana da  Ingilishi wadanda suke zargin ana ci da guminsu. To amma Barista Suley Zakari lauya mai zaman kanshi da ke birnin Bamenda a Arewa maso yammacin kasar Kamaru ya ce kafin a aiwatar da hukuncin kisa akwai tsauraran matakai da dokokin kasar ta Kamaru suka tanada.

A cewar masu fafutikar kare hakin bil-Adama na kasa da kasa, kasashen da ke aiwatar da wannan hukunci na kisa ya kyautu sun canza dubara wajen samar da hanyoyin da za su tilasta bin dokoki tare da kara yawan 'yan sanda da basu kayan aiki, da kuma samar wa kotuna kayayakin aiki na zamani.