Ahmedinejad ya musanta cewa Iran na baiwa yan takifen Iraqi makamai | Labarai | DW | 12.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ahmedinejad ya musanta cewa Iran na baiwa yan takifen Iraqi makamai

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya musanta zargin da Amurka ke yi cewa Iran ce ke baiwa yan takifen Iraqi muggan makamai. Yace zaá sami maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kawai a Iraqi idan sojojin Amurka da kawayen ta na kasashen ketare suka tatttara yana su ya nasu suka fice daga Iraqi.

Ahmedinejad yace gwamnatin Amurka da shugaba George W Bush babu abin da suka sa a gaba sai zargi da sukar lamirin wasu kasashe. A jiya lahadi sojin Amurka a birnin Bagadaza suka gabatar da abin da suka baiyana da cewa babbar shaida ta makaman Iran da yan takife ke amfani da su wajen kashe sojojin Amurka. Jamiaán sun gabatarwa yan jarida bangorin makamai kirar kasar Iran, suna mai cewa manyan jamián gwamnatin Tehran na da hannu dumu dumu wajen baiwa yan takifen makamai.