Afrika ta Kudu na son karin lokaci daga kotun ICC kan tsafke Shugaban Sudan. | Labarai | DW | 05.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afrika ta Kudu na son karin lokaci daga kotun ICC kan tsafke Shugaban Sudan.

Kasar Afrika ta kudu ta bukaci kotun ta kasa da kasa wato ICC data basu karin lokaci don bayar da bayanai kan yadda aka yi suka bar Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ficewa daga kasar ba tare da sun kama shi ba.

Tun dai shekara ta 2009 kotun dake da mazau nin ta a birnin Hague ta bayar da takardar sammacen kamo Omar al-Bashir a bisa zarge-zargen kisan kiyashi gami da take hakkokin bil Adama a yayin rikicin yankin Darfur na kasar.

Kasar Afrika ta kudu wacce tayi na'am da tande tanaden kotun ta Icc tare da bugar kirgin aiwatar da sammacen to amma ta gaza tsafke Al Bashir a yayin taron shugabanin kasashen Afrika daya gudana a kasar.

Yanzu haka dai mahukuntan Afrikan ta kudun sun ce zasu tinkari kotun ta ICC don neman karin lokacin yin bayanai dalla dalla.