Afirka ta Kudu: Najeriya za ta kwashe ′yan kasar | Labarai | DW | 09.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu: Najeriya za ta kwashe 'yan kasar

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta soma aikin kwashe 'yan kasar daga Afrika ta Kudu a cikin wannan makon bayan da aka gagara shawo kan rikicin kin jinin baki.

Jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu Godwin Adamu ne ya sanar ma kamfanin dillancin Labaran Faransa AFP matakin da gwamnatin kasar ta dauka, na kwashe mutum akalla dari shida (600) a wannan makon. Jirgin farko na kamfanin Air Peace, zai tashi ne a ranar Laraba da mutum dari uku da shirin (320) injin jakadan.

Rikicin kin jinin baki da Afrika ta Kudu ta yi kaurin suna a kai, ya kara kamari inda 'yan Najeriya suka kasance mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya shafa asarar rayuka da dukiya a hargitsin na baya-bayan nan. Wasu 'yan Najeriya sun mayar da martani tare da  lalata kamfanoni mallakin Afrika ta Kudun da ke a sassan kasar.