Afirka a Jaridun Jamus: 22.05.2020 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 22.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus: 22.05.2020

Murabus din firaministan Lesotho da babban zaben kasar Burundi da kuma batun coronavirus a kasashen Senegal da Tanzaniya, na daga cikin batutuwan Afirka da suka dauki hankulan masu sharhi a jaridun Jamus na wannan makon.

Lesothos Premierminister Thabane

Firaministan Lesotho da ya yi murabus, Thomas Motsoahae Thabane 

Karshen kikikar siyasar Lesotho ya zo. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta rubuta. Jaridar ta ce firaminista mai shekaru 80 a duniya, ya gaza, dangane da haka ya nemi masarautar kasar ta sauwake masa. A cewar Thomas Motsoahae Thabane a yanzu ba shi da kuzarin ci gaba da mulkin kasar mai yawan al'umma miliyan biyu. Daga wannan Jumma'ar kakakin firaministan ya ce Thabane zai ajiye muklaminsa. Da ma dai tuni farin jinin firaministan ya yi matukar dushewa, inda wasu 'yan majalisar dokokin kasar suka fito fili suna neman sai ya yi murabus.

Burundi Wahlkampf Präsident Pierre Nkurunziza

Pierre Nkurunziza bai yi takara ba

A nata sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bayyana cewa a Larabar wannan makon aka gudanar da zabe a kasar Burundi. Jaridar ta ce akwai manyan abubuwa biyu da ke tattare da zaben na Burundi. Na farko dai zaben ya gudana cikin yanayin barazanar annobar COVID-19, na biyu kuwa shi ne, an gudanar da zaben a karon farko shugaba Pierre Nkurunziza ba ya cikin 'yan takara. Duk da cewa tun sama da shekara guda bayan da ya take dokar kasar ya ci gaba da mulki, amma daga karshe dai zai ajiye mukamin.

An kusa yakin basasa

A tsukin shekarar da ya yi bayan kin bin dokokin kundin tsarin mulki na hana ta zarcen wa'adi na uku, kasar Burundi ta kusan fadawa cikin yakin basasa, inda akalla mutane 1000 suka rasa rayukansu a tarzomar bayan zaben. Bayan sauya tsarin mulki da ke cike da takaddama, an yarda Nkurunziza ya mulki kasar har zuwa shekara ta 2034, amma kwatsam sai ya sanar da cewa ba zai yi takara a bana ba, abinda ya kawo karshen mulkin da ya hau tun shekara ta 2005.

Senegal Dakar | Pflegepersonal | Pikine Hospital

Rayuwa bayan coronavirus

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta yi sharhinta ne kan yadda rayuwa ta fara dawowa a kasar Senegal. Jaridar ta fara da cewa bayan da annobar cutar corona ta mamaye kasar wanne darasi aka koya, kuma yanzu da rayuwa da sauran walwalar jama'a ta fara dawowa sai me za a duba? Jaridar wacce ta yi hira da fitaccen mawakin kasar Sengal  Rapper Thiat ta duba yadda kungiyoyi masu zaman kansu na 'yan fafutaka suka bayar da kyakkyawar gudummawa wajen yakar COVID-19. Kasar Senegal ta yi fice a Afirka wajen samun matasa da suka hada hannu da gwamnati a yaki da annobar cutar ta coronavirus.

Me ake ciki a Tanzaniya?

Shi kuwa shugaban kasar Tanzaniya ya sallami babban jami'in kula da cibiyar gwajin cututtukan na kasar a cewar jaridar. Shugaban na Tazaniya ya ce ya gaji da ganin duk wanda aka gwada sai ace yana da cutar coronavirus. Tun ranar da aka sallami wannan babban daraktan cibiyar gwajin, ba a kara samun wani da ke dauke da cutar COVID-19 ba, domin babu damar samun alkalumman, kasancewar babu jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, da aka bari a kasar. Hakan ta sa tun farkon watan Mayun da muke ciki, ba wanda ya bayar da labarin halin da ake ciki kan annobar a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin