Afirka a Jaridun Jamus 06.11.20 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 06.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus 06.11.20

Rikicin da ake fama da shi a kasar Habasha da siyasar kasar Côte d'Ivoire da kuma zaben da aka yi a Tanzaniya sun dauki hankulan jaridun Jamus.

Jaridar Süddeutsche Zeitung da ta rubuta sharhinta mai taken Hasha cikin rudani. Firaminista Abiy Ahmed ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, sai dai yanzu yana amfani da sojoji wajen kokarin dakile 'yan adawa. Jaridar ta ce shekara guda ke nan da dan Afirkan da ya yi kokarin kawo gyara Firaminista Abiy Ahmed ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel . Sai dai a yanzu yana neman bata rawarsa da tsalle, domin kuwa firaminstan na Habasha Abiy Ahmed na amfani da sojoji wajen yin abin da ya bayyana da ceton kasarsa daga masun kokarin tarwatsa ta. Kasar da ke yankin kahon Afirka, na shirin fada wa cikin yakin basasa. Shugaban gwamnatin Abiy ya dora alhakin hakan a kan mayakan 'yan tawayen Tigray da ke yankin arewacin kasar. Yana zarginsu da kaddamar da hari a kan sansanin sojojin gwamnati, harin kuma da ya halaka mutane masu yawa, inda ya yi zargin cewa sun yi kokarin kwace manyan makamai daga hannun sojojin. Da wannan matakin Abiy Ahmed ya nunar da cewa ba zai iya jure hakan ba, kuma a ganinsa matakin mayar da martani da karfin soja shi ne abin da ya dace. Mai shekaru 44 a duniya, Abiy na fuskantar babban kalubale na lokacin mulkinsa.

Karin Bayani: Ra'ayin 'yan Habasha kan salon mulkin Abiy

Matakin sojan da ya dauka dai ka iya rura wutar rikici a kasar ta yankin Kahon Afirka. A shekara ta 1999 'yan tawayen na Tigray sun kifar da gawamnatin mulkin soja ta wancan lokaci, kuma tun daga lokacin al'ummar yankin ke samun damar darewa kan karagar mulki, kafin Abiy Ahmed da ya fito daga yankin Oromia da kuma ke fatan kawo sulhu a rikicin kasar ya samu nasarar zama firaminista a shekara ta 2018. 

Nasarar jeka na yi ka a zaben Côte d'Ivoire

Nasarar jeka na yi ka ga Alassane Ouattara inji jaridar die tageszeitung. Shugaban kassar ya lashe zabe da kaso 94 cikin 100, bayan da 'yan adawa suka kauracewa zaben baki daya, 'yan adawar dai sun nuna kin amincewa da nasarar tasa, kuma suna son kafa tasu gwamnatin. Jaridar ta ce hukumar zabe a Côte d'Ivoire ta kwashe tsawon lokaci kafin ta bayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 31 ga watan Oktobar da ya gabata. Sai a Alhamis din wannan makon ne dai hukumar zaben ta bayyana cewa Ouattara ya lashe zaben da kaso sama da 94 cikin kuri'un da al'ummar kasar sama da miliyan uku suka kada. Duk da cewa sun kauracewa zaben, jagororin adawar Henri Konan Bédié da Pascal Affi N’Guessan sun samu kimanin kuri’u dubu 85. Sun dai bayyana cewa kiran nasu na a kauracewa zaben ya samu nasara a zaben Côte d'Ivoire, kasancewar ya yi mummunan tasiri ga zabukan da aka gudanar. A ranar Litinin, sun sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagoran cintsohon shugaban kasar Bédié da ke da shekaru 86 a duniya. Masu sanya idanu a zaben a ciki da wajen kasar  dai, sun yi kakkausar suka dangane da yadda aka gudanar da zaben.

Fatali da sakamakon zaben Tanzaniya

 Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi nata sharhin ne kan zaben da aka gudanar a kasar Tanzaniya. A sharhinta mai taken Suka kan zaben kasar Tanzaniya, 'yan adawa ba su amince da nasara da Shugaba Magufuli ya samu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da aka gudanar ba. Jaridar ta ce 'yan adawa a Tanzaniya sun yi fatali da sakamakon zaben shugaban kasa da ya bai wa Shugaba John Magufuli damar yin tazarce . Sakamakon zaben dai ya bayyana cewa Shugaba Magufuli ya samu nasara da kaso 84 cikin 100 na kuri'un da al'ummar kasar kimanin miliyan 14 suka kada. Yayin da abokin hamayyarsa Tundu Lissu ya samu kaso 13 cikin 100. Tun ma gabanin hukumar zaben kasar ta bayyana sakamako a ranar Jumma'ar makon da ya gabata, Lisu ya bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa abin da aka gudanar a ranar Laraba 28 ga watan Oktoban da ya gabata ba zabe ba ne. Masu sanya idanu a zaben na ciki da wajen kassar, kamar ofishin jakadancin Amirka a Tanzaniyar, sun bayyana tantama dangane da sakamkaon zaben da suka ce an gudanar da shi cikin firgici da takura. Mai shekaru 61 a duniya, Magufuli ya samu nasarar darewa kan karagar mulkin kasar tun a shekara ta 2015.