1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shrhin jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
December 4, 2020

Kisan da aka yi wa manoma a Najeriya da rikicin yankin Tigray a kasar Habasha sun zama lamuran Afirka da suka mamaye jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3mF84
Nigeria Region Borno Boko Haram
Kisan gilla mai muni a kan manoma a NajeriyaHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka Najeriya tana mai cewa an yanka manoman shinkafa kamar yadda ake yanka dabbobi. Ta ce a wani kisan gilla mafi muni a wannan shekarar da ake zargin mayakan Boko Haram da aikatawa, kimanin mutane 110 aka halaka a wata gonar shinkafa da ke garin Zabarmari mai tazarar kilo-mita 25 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke Najeriya. Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya jagoranci jana'izar da aka yi wa manoma 43  a ranar Lahadi, sannan da yammacin wannan rana aka tabbatar da yawan wadanda aka yi wa yankan ragon ya karu zuwa mutane 110. Jaridar ta ce a kullum gwamnatin Najeriya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari na ikirarin cewa ta yi nasara kan 'yan ta'adda, amma abin da ke faruwa a zahiri na karyata wannan ikirari. Saboda haka ne wasu kungiyoyin farar hula a Najeriyar, suka yi kira ga shugaban da ko dai ya sallami hafsoshin tsaron kasar da na hukumomin leken asiri da na 'yan sanda nan-take ya kuma yi wa hukumomin tsaron garambawul ko kuma ya yi murabus.

Äthiopier Flüchten vor Kämpfen in Tigray in den Sudan
'Yan gudun hijirar Habasha na cikin taskuHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Daga rikicin Boko Haram a Najeriya sai kuma rikicin yankin Tigray a kasar Habasha, inda jaridar Neues Deutschland ta yi tsokaci tana mai cewa rikicin da ake yi a yankin Tirgay ya tsananta halin da 'yan gudun hijirar Iritriya ke ciki. Ta ce shingen da ke hana iyalan 'yan gudun hijirar Iritriya zuwa Jamus ya yi tsayi sosai. Da ma mata da kananan yara da ke cikin mawuyacin hali a kasashe makwatan Iritiriya musamman Habasha da Sudan da Kenya da kuma Yuganda suna cikin barazana, yanzu kuma ga rikicin kasar Habasha ya kara jefa su cikin halin ni 'yasu kasancewa suna cikin tsakiyar yankin da ake gwabza yaki, a cewar 'yan gudun hijirar Iritiriya da suka yi wannan gangami a gaban ma'aikatar harkokin wajen Jamus da ke birnin Berlin. Sun yi kira ga hukumomin Jamus da su saukaka hanyoyin dauko iyalansu da suka nemi mafaka a dab da iyakar yankin Tigray da ake rikici tsakanin kungiyar kwatar 'yancin kan yankin da gwamnatin tsakiya ta birnin Addis Ababa. Tsawon shekaru 'yancin ba wa iyali shigowa na hannun ofisoshin jakadancin Jamus a ketare, amma sau da yawa ana tababar sahihancin takardun da iyalan ke gabatarwa jami'an diplomasiyyar Jamus din. Saboda haka ake daukar lokaci kafin samun takaddun izinin zuwa Jamus daga iyalan 'yan Iritiriya da ke gida.

Eco Africa Sendung Südafrika
haihuwa ba tazara kan cutar da yara da uwa

A karshe sai jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan mako ta yi sharhi ne a kan batun tsarin iyali ko ba da tazarar haihuwa, batun da ake cece-kuce kanshi a da yawa daga cikin kasashen Afirka. Ta ce yayin da yawan haihuwa ke raguwa a duniya, a kasashen Kudu da Saharar Afirka, babu sauyi. Kowace mace kan haifar yara biyar, a yammacin Afirka ya kai yara shida. Idan aka ci gaba kamar yadda ake yanzu, yawan mutane a Afirka zai ninka sau biyu zuwa mutum miliyan dubu biyu da miliyan 500 kafin shekara ta 2050. Ko da yake ana samun bunkasar tattalin arziki a nahiyar, amma bunkasar jama'ar na hadiye ci-gaban tattalin arzikin, wanda hakan ke nufin yawan masu fama da matsalar talauci zai ci gaba da karuwa.