Hukumar NFF ta sanar da jerin 'yan kwallo 28 da za su buga mata wasan AFCON a Kamaru, ciki har da Ahmed Musa da Kenneth Omeruo wadanda ke cikin 'yan wasan kasar a shekara ta 2013, lokacin da Najeriya ta lashe gasar.
Hukumar Kwallon Kafar Najeriya, NFF ta sanya dan wasa Victor Osimhen, dan kasar da ke buga wa kungiyar Napoli ta Italiya a cikin 'yan wasan da za su kare mata mutunci a fafatawar da za a yi da ita a gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON.
Victor Osimhen na cikin hutunsa na watanni uku a Napoli ne bayan wani rauni da ya samu a watan Nuwamba a fuskarsa. Amma tun a farkon makon nan aka gan shi yana atisaye, sannan ya wallafa cewa yana fatar zai shiga cikin 'yan wasan da za su buga wa Najeriya a gasar ta AFCON wace ake sa ran gudanarwa a watan gobe na Janairu a kasar Kamaru.