AEC: Za a yi sabon zama kan kasar Burundi | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AEC: Za a yi sabon zama kan kasar Burundi

Shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka na EAC, za su gudanar da taron koli don tattauna matsalar kasar Burundi mako daya bayan zaben da ya gudana a wannan kasa.

Kamar sauran da suka gudana na baya a ranakun 13 da kuma na 31 ga watan Mayu da ya gabata, shi ma wannan taron na shugabannin kasashen Gabashin na Afirka zai gudana ne a birnin Dar Es-Salaam na kasar Tanzaniya, inda shugabannin za su yi bitar halin da ake ciki kan rikicin kasar Burundi tun bayan tarurukansu na baya.

Kasashen dai sun hada da kasar ta Burundi, Tanzaniya, Ruwanda, Yuganda da kuma Kenya wadanda kamar sauran kasashen duniya da ma manyan kungiyoyi irin su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka, ke neman a dage zabukan kasar ta Burundi ya zuwa 30 ga watan nan na Yuli.