1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adduo'in rahama ga mutanen da suka rasu a ta'asar Norway

July 24, 2011

Basaraken Norway sarki Harald da matarsa sarauniya Sonja na daga cikin mashahuran mutanen da suka halarci adduo'i domin neman rahama ga mutanen da suka rasu a harin da ya hallaka mutane 93.

https://p.dw.com/p/122aP
Taron addu'oi a wata mujami'a a ƙasar Norway.Hoto: dapd

A ranar lahadin nan ce aka gudanar da addu'oi na musamman a mujama'ar Oslo a ƙasar Norway domin neman rahama ga mutanen da suka rasu a ta'asar harin ta'ddanci. Taron adduo'in ya sami halartar basaraken ƙasar sarki Harald da matarsa sarauniya Sonja da Ministoci da kuma 'yan siyasa. Shima Paparoma Benedict na 16 ya baiyana jimaminsa ga mutanen da ta'asar harin ta rutsa da su wanda ya hallaka mutane 93.

Norwegen Anschläge Juli 2011 Trauer
Jimamin mutanen da suka rasu a ta'asar Norway.Hoto: dapd

Da yake jawabi a lokacin addu'oin Firaministan ƙasar ta Norway Jens Stoltenberg ya baiyana harin a matsayin aljabi mai ɗaure kai. Yace nan ba da jimawa ba za'a wallafa sunaye da hotunan mutanen da suka rasu. Ya shaidawa jama'ar ƙasar cewa ɗaukacin al'umar duniya na taya su juyayin wannan abin baƙin cikin da yaa faru, inda ya miƙa ta'aziyar shugaban Amirka Barack Obama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma na sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon.

Shima a nasa ɓangaren Paparoman ya baiyana jimamin ne yayin adduo'in da ya saba yi na mako mako daga gidansa dake Gandolfo a ƙasar Italiya. Ya kuma yi kira ga dukkan al'uma su yi watsi da tafarkin ƙiyayya da gaba domin kuɓuta daga sharrin shaiɗan. A ranar litinin ne kuma za'a gurfanar da ɗan bindigar da aka cafke mai suna Anders B a gaban kotu wanda da ya yi iƙarin aikata ta'asar harin bam ɗin da kuma harbin bindiga.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu