Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Norway kasa ce da ke yankin nan na Skandaneviya, sai dai ba ta cikin jerin kasashen da ke karkashin Kungiyar Gamayyar Turai.
Ta na da makwabtaka da Rasha da Swenden da Finland. Gidan sarautar kasar ya na daga cikin wadanda suka jima a Turai.
Ministan tsaron Norway Bjørn Arild Gram ya sanar da cewa, kasarsa za ta aika da tankokin yakin nan kirar Leopard 2 guda takwas ga Ukraine, domin kara taimaka mata a yakin da take da Rasha.
A wannan Litinin aka bude babban taron kasa da kasa a birnin Yamai na kasar Nijar don nazari kan yadda za a sake gina yankin Tafkin Chadi da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Wakilai na yankin Tafkin Chadi da na kasashen Jamus da Norway sun hadu a Nijar don nazarin hanyoyin sake gina yankin da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Wasannin olympics na lokacin sanyi sun kammala a birnin Beijing, inda Noway da Jamus da Chaina suka fi samun lambobi. Muna tafe da sakamakon wasannin Bundesliga na Jamus.
Shugaban Kiristoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Francis ya yi tir da hare-haren da aka kai da suka yi sanadiyar rayuka a kasashen Norway da Britaniya da kuma Afghanistan.
'Yan sandan Kongsberg a yammacin Oslo sun kama mutumin da ya kashe mutane biyar da kibiya, amma an ce ba da jimawa ba za a bayyana ko harin na da nasaba da ta'addanci.
'Yan sanda a kasar Norway, sun ce wani dan bindiga dadi dauke da makamai, ya buda wuta kan masallata a kusa da Oslo babban birnin kasar.
Wakilan gwamnatin Venezuela da bangaren adawa za su gana a tsibirin Barbados domin fara tattauna batun kawo karshen rikicin siyasar kasar da ya ki ci yaki cinyewa.
Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela, ya yi marhabin da shirin da kasar Norway ta bijiro da shi na tattaunawa tsakaninsa da madugun adawar kasar Juan Guaido.
Kasar Jamus za ta aika da wakilci lokacin wani atisayen sojin kungiyar tsaro ta NATO da za a yi a kasar Norway.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway, ta nuna damuwa kan yadda hukumomi suka gaza kawo karshen yaki da ke halaka fararen hula a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A cikin shirin za a ji cewa kasar Norway ta kasance mafi farin cikin al'umma a duniya. Mun leka Kaduna garin gwamna a Najeriya da kuma Damagaram a Jamhuriyar Niger domin jin abin da ke sanya al'umma farinciki. Can kuwa a Kamaru tashin hankali na ci gaba da gudana a yankin kasar da ke amfani da Ingilishi.
Ranar farin ciki ta duniya rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin waiwaye kan farin cikin al'umma da wadatar arziki da wanzuwar cigaba mai ma'ana da kuma kawar da talauci a tsakanin al'umma.
An samu matukan jirgin na kamfanin jiragen sama na Lettone Air Baltic sun yi tatul barasar da ta wuce kima a lokacin da suke shirin daukar fasinja.
Malala Yousoufzai 'yar asaslin Pakistan da Kailash Satyarthi dan asalin Indiya sun sami lambar yabon ne sakamakon fafutukar da suke yi wajen ganin sun kyautata makoman kananan yara
Anders Behring Breivik ya amsa laifin kashe mutane 77 a kasar Norway a watan Yulin shekarar 2011