Adawa da dokar yakar ta′addanci a Kamaru | Siyasa | DW | 09.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Adawa da dokar yakar ta'addanci a Kamaru

Kungiyoyin masu zaman kansu da jam'iyyun adawa na shirin gudanar da zanga-zanga domin tilasta gwamnati gyara dokar da ta shafi ta'addanci da majalisa ta amince da ita.

Hukuncin kisa dai na daga cikin shika-shikan dokokin kasar Kamaru tun shekaru da dama da suka gabata. Amma kuma ana yankeshi a kan mutumin da aka samu da laifin kisan kai ko kuma cin amanar kasa. Sai dai kuma rintsabewar da al'amuran tsaro suka yi a arewacin kasar sakamakon hare-haren kungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram, ya sa majalisun wakilai da na dattawa fadada dokar. Alal hakika ma dai daga yanzu za a kashe duk wani ko watan da aka samu da hannu a ayyukan da suka shafi ta'addanci. Hasali ma dai wannan doka za ta shafi duk wanda ya samu horo daga kasar waje da kuma wanda aka gama kai da shi da nufin tayar da zaune tsaye.

Sai dai kuma inda gizo ke saka shi ne, dokar na bayar da damar yanke hukuncin kisa a kan duk wanda ya yayata ko ya kuruta ayyukan ta'addanci ko a Kamaru aka gudanar da shi ko kuma a kasashen ketare ne. Lamarin da kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida suka ce ba za ta sabu ba, saboda tana karar tsaye ga aikinsu na bayyana wa al'uma zahirin abin dake faruwa. Sannan kuma ta shafi wadannan za su gudanar da gangami ko kuma zanga-zanga ba tare da samun izini daga hukumomi.

Kamerun Präsident Paul Biya Archivbild 30.01.2013

Shugaba Paul Biya na Kamaru

Barista Jean de Dieu Momo wanda dan rajin kare hakkin bil Adama ne kana shugaban jam'iyyar adawa ta PADEC ya ce, gwamnatin Kamaru na neman yin rigakafi wanda ya fi magani dangane da duk wani yunkurin na gudanar da zanga-zangar neman sauyi, shigen na kasashen Larabawa da kuma Burkina Faso.

"Abu ne mai kyau ace an dauki matakai a kan yayyukan ta'adanci. Amma kuma hankali ba zai dauka ba idan aka ce an fadadashi a kan zanga-zangar da 'yan kasa da za su gudanar domin neman a biya musu wasu bukatunsu. Wannan dai ya nuna cewar gwamnati kasarmu na neman dakile irin guguwar neman sauyi da ta kada a Burkina Faso."

A baya dai gwamnatocin Ahmadu Ahidjo da kuma ta Paul Biya sun ta yin amfani da dokar 1962 wajen daure wasu 'yan boko da kuma 'yan siyasa da ba sa dasawa da su a gidajen yarin kare kukarka na Tchollire de mantoum da kuma Yoko. Sai dai kuma ita gwamnati mai ci yanzu ta ce maganar yin bita da kullin siyasa ma ba ta taso ba. Babban abin da ta sa a gaba dai shi ne, kare 'yan kasar daga barazanar tsaro a gabashi sakamakon rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma a arewaci sakamkon hare-haren Boko Haram. A wannan fannin Momo ya ce dokar ta yi daidai.

Sauti da bidiyo akan labarin