Adadin ′yan gudun hijira ya kai miliyan 80 | Labarai | DW | 18.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adadin 'yan gudun hijira ya kai miliyan 80

Wani rahoton da MDD ta wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewa adadin mutanen da tashe-tashen hankula suka tilasta wa shiga gudun hijira ya kai miliyan 80 wato kaso daya cikin dari na al'ummar duniya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da tashe-tashen hankula da yake-yake da ma take-taken hakkin dan Adam ke cilasta wa barin gidajensu ya karu fiye da kima inda ya kai a halin yanzu kimanin mutane miliyan 80 wato kaso daya daga cikin dari na al'ummar duniya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton da ta wallafa a wannan Alhamis inda ta ce a karshen shekara ta 2019, mutane miliyan 79 da rabi ne ke zaman gudun hijira, daga cikinsu sama da miliyan 45 'yan gudun hijira ne na cikin gida wadanda sun tsere daga garuruwansu na asali zuwa wasu garuruwan kasar tasu na dabam, a yayin wasu miliyan 26 sun kuwa sun tsere daga kasarsu ta asali zuwa kasashe makobta.

Rahoton ya ce kaso 68 daga cikin dari na mutanen da suka tseren daga gidajen nasu sun fito ne daga kasashen biyar na Siriya da Venezuwela, Afganistan Sudan ta Kudu da kuma Bama.