Adadin wadanda suka rasu a sansanin Dikwa ya karu | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adadin wadanda suka rasu a sansanin Dikwa ya karu

Mutane 58 ne suka rasu wasu kuma 78 suka samu raunuka sakamakon tagwayen hare-haren kunar bakin wake na sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa a Jihar Borno.

Babban jamiin hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya ya tabbatar da wannan adadi, inda ya ce a halin yanzu wadanda suka jikkata na can suna samun kulawa a asibitoci. 'Yar kunar bakin waken ta uku dai ta ki amincewa ta tayar da bam din da ke jikinta, bayan da ta yi la'akkarin cewa a kwai uwayanta da sauran danginta cikin wannan fili, inda daga bisani ta mika kan ta ga hukumomi.

Akwai dai sama da mutane dubu hamsin da ke zaman gudun hijira a wannan sansani kuma yawancin su sun fito ne daga kanan hukumomin Ngala da Kala Balge da Dikwa da Mafa da Marte da karamar hukumar Bama duk a jihar Borno. Wadan nan sabbin hare-hare na tayar wa mazauna yankin hankali a lokacin da suka fara sakin jiki tare da fatan da suke na komawa garuruwan su ba da dadewa ba.