Jami'an 'yan sanda a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja sun harba harsashen gaske kan mabiya tafarkin Shi'a a kokarinsu na tarwatsa wata zanga-zanga da suka fito yi.
'Yan shi'a sun fito zanga-zangar ce don kira ga mahukuntan Najeriyar da su saki shugabansu da suke tsare da shi tun shekarar 2015 tare kuma da yin tir da kalaman da gwamna jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi na cewar mudin yana kan kujerar mulkin jihar ba za a saki shugaban na su ba.
Mai magana da yawun mabiya tafarkin na Shi'a ya sanar cewar harbin ya sami mutane biyar wanda biyu daga cikinsu 'yan kungiyarsu ne. Ya kara da cewar sun fito ne su. Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriyar ta bakin kakinta da ke Abuja Anjugurl Manza ya musanta harbin 'yan Shi'ar.