Abu Namu: Zamantakewar aure a kasar Hausa | Zamantakewa | DW | 14.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu Namu: Zamantakewar aure a kasar Hausa

Wasu jihohin arewacin Najeriya sun sha hobbasa don shawo kan matsalar mace-macen aure, inda suka bijiro da shirin aurar da zawarawa amma kawo yanzu ba ta sauya zane ba.

Saurari sauti 10:00

Matsalar mace-macen aure a kasar Hausa na kara kamari: Wasu jihohin arewacin Najeriya sun sha hobbasa don shawo kan wannan annoba inda suka bijiro da shirin aurar da zawarawa sai dai kawo yanzu babu wani canji na a zo a gani.

Shirin na wannan mako zai mayar da hankali kan yankin Hausawa a Najeriya inda akasarinsu suka kasance mabiya addinin Musulunci.