1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Abu Namu: 'Yancin mata a kasashen Larabawa

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
March 9, 2020

Yarima mai jiran gadon kasar Saudiyya, Muhammad Bin Salman na ci gaba da daukar matakan kyale matan kasar su sakata su wala, sabanin a baya da matan kasar da ma duniya baki daya ke nan 'yancin mata a Saudiyya na cikin tasku. 

https://p.dw.com/p/3Z54T

A kowacce ranar takwas ga watan Maris ake gudanar da bikin ranar mata ta duniya, da nufin bayyana 'yancin da matan ke da su da kuma yakar abubuwan da suka danganci take musu hakkokin nasu. Taken bikin na bana shi ne: "Daidaita 'Yanci ga Kowa". Dangane da hakan, shirin na wannan lokaci zai yi nazari kan batun 'yancin mata a wasu kasashen Larabawa inda za mu isa kasar Saudiyya domin jin yadda Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman ke ci gaba da daukar matakan kyale matan kasar su sakata su wala, sabanin a baya da matan kasar da ma duniya baki daya ke ganin 'yancin mata a Saudiyya na cikin wani wadi na tsaka mai wuya.