Aikewa da yara neman ilimin addini
May 6, 2019Talla
Almajiranci dai shi ne yanayin da iyayen yara kan kwaso 'ya'yansu daga wata uwa duniya su na kai wa wasu garuruwan masu nisa da nufin su yi karatun allo wato su sauke Al'kur'ani.
Sai dai abin takaici sau tari yaran kan tashi a tutar babu, ba su samu ilimin ba kuma su fuskanci matsaloli na rayuwa wasu lokutan ma su kan rasa rayukansu. Ko ta wacce hanya za a shawo kan wadannan matsalolin?
Wannan batu ne dai shirin ya yi nazari a kai inda muka ji ta bakin almajiran da masu fafutukar kare hakkinsu da kuma malamin addinin Musulunci.