1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Mata masu matsa wa mazajensu lamba

July 10, 2023

A Najeriya daruruwan mazaje ne ke fuskantar cin zarafin irin dabam-dabam a wajen matansu, wanda hakan ke saka da dama daga cikinsu cikin kunci na rayuwa wani lokaci ma har su rasa lafiyar su.

https://p.dw.com/p/4TgZ0
Hoto: Daniel Plafker/DW

Cin zarafin maza da mata ke yi a Najeriya ya zama ruwan dare inda kusan ko' ina kaje a kasar ana cin zarafin maza, duk da irin wa’azi da malamai da wasu iyaye ke yi ga matan da su bi mazajensu. Amma duk da hakan wasu matan sun yi watsi da hakan. Sai ka ga wata mace har wani tinkaho da nuna isa ta ke yi in tana musgunawa mijin ta musamman ma ina ana kiran shi da mijin hajiya.