1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na fafutukar neman na dogaro da kai

July 12, 2021

Ci gaban da aka samu a zamantakewar aure ta fannin yadda mata suka tashi haikan a yanzu don neman na kai domin jin dadin rayuwa misali a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3wMt8
Symbolbild Afrika Markt Bunt
Hoto: P. U. Ekpei/AFP/Getty Images

 
Tun dai a wancan zamanin da duniya ke kwance ake kiran mata da su kama sana'a. A kan ce rashin sana'a ga mace shi ke kawo yawan fadace-fadace tsakanin uwargida da mai gida, ta yiwu yawan bani-bani daga bangaren matar gida a kan kudin cefane ko kudin anko ko dai wani abu da ya shafi na hidimomin yau da kullum. Sai dai da dama na ganin an sami ci gaba sosai na yawaitar samun yawan sabani tsakanin ma'aurata saboda yadda mata a wannan lokacin suke fadi tashin ganin sun mayar da taro zuwa sisi wanda ke ba su damar dauke kananan dawainiya da ya shafe su ko 'ya'yansu, kuma matan ke cewa hakan ya sa mazajensu yin alfahari da su.