1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Abu Namu: Kawalci a arewacin Najeriya

Zulaiha Abubakar MNA
January 27, 2020

A wannan makon shirin na Abu Namu ya duba yadda kawalci ya fara samun gurin zama a arewacin  Najeriya, munin al'amarin ya kai maza magidanta na tsalleke iyalansu, su tare a otel don sharholiya

https://p.dw.com/p/3Wrh3

'Yan mata da samari da dama sun tsinci kansu a wannan yanayi ko dai sun kai kansu ko kuma abokai ko kawaye ko rashin sanya ido daga bangaren iyaye ya jefa su a shiga kawalci.


Hidimonin yau da gobe irin na duniyar yanzu, sun dauke hankulan iyaye da dama game da irin wainar da 'ya'yansu ke toyawa, a wani bangaren kuma bazuwar kafofin sadarwar zamani ya sanya wasu 'ya'yan na yiwa iyaye da majibantan lamuransu ungulu da kan zabo cikin sauki. Ganin yadda wannan al'ada ta samu gurin zama, shirin ya duba yadda wasu matasa a Najeriya suka mayar da kawalci sana'a.