Abu Namu: Kalubalan rayuwar mata zawarawa a kasar Hausa | Zamantakewa | DW | 27.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu Namu: Kalubalan rayuwar mata zawarawa a kasar Hausa

A kasar Hausa, matan da ke rayuwar zawarci bayan rasa aurensu a bisa dalili na mutuwar aure ko mutuwar miji na fuskantar a wasu lokuttan kalubalai na tsangwaman da ma zargi daga danginsu da sauran al'umma.

Sakamakon yadda wasu daga cikin matan da aurensu ya mutu ke fuskantar kunci daga irin kallon da al'umma ke yi musu ciki kuwa har da mata 'yan uwansu, da dangi da kawaye, idan ba an yi dace da iyaye ko 'yan uwa masu sassauci da rungumar kaddara ba, macen da aurenta ya mutu ta kan shiga wani yanayi na rana zafi inuwa kuna.

Sauti da bidiyo akan labarin