1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Abu Namu: Cin zarafi da mace-macen aure a Arewacin Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
February 17, 2020

A Arewacin Najeriya na samu wani miji da ya daure matansu su biyu ya ci kuma zarafinsu na tsawon wani lokaci kafin a samu nasarar ceto su.

https://p.dw.com/p/3Xsdr

A wannan lokaci shirin na Abu Namu ya yi nazari kan yadda ake samun cin zarafi da musgunawa da kuma mace-macen aure musamman a yankin Arewacin Najeriya. Mafi akasari dai ana danganta matsalolin da ake samu a gidajen aure da kaucewa turbar da aka amince a nemi auren tun asali, wasu kan ce ana gina auren a kan karya yayin da wasu ke ganin ai laifin ma na iyaye ne, domin su ne ba sa gudanar da binciken da ya dace gabanin su aurar da 'ya'yansu ko kuma su nema musu aure, ma'ana daga mazan har matan akwai matsala idan aka zo batun yin bincike gabanin aure.