A yau ne Bosco Ntaganda zai gurfana gaban kotu ICC | Labarai | DW | 26.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ne Bosco Ntaganda zai gurfana gaban kotu ICC

A wannan Talatar ce Bosco Ntaganda zai gurfana a gaban kotun hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa saboda zargin sa da ake da aikata laifukan yaki.

Fugitive Congolese warlord Bosco Ntaganda attends rebel commander Sultani Makenga's wedding in Goma December 27, 2009. Ntaganda walked into the U.S. Embassy in Rwanda on March 18, 2013 and asked to be transferred to the International Criminal Court, where he faces war crimes charges racked up during years of rebellion. Picture taken December 27, 2009. REUTERS/Paul Harera (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: CIVIL UNREST CRIME LAW MILITARY POLITICS SOCIETY)

Bosco Ntaganda

Ana dai zargin Mr. Ntaganda ne da aikata laifukan da su ka danganci kisan kai da fyade da kuma tursasawa yara kanana shiga aiki soji a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo.

Yayin zaman kotun za a fara ne tabbatar da mutumin a matsayinsa na Bosco Ntaganda, daga bisani kuma a karanto masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa kana a tantance harshe da zai fi fahimta yayin shari'ar sannan a karshe a dage zaman kotun zuwa wani lokaci da a za a fara sauraron karar.

A makon jiya ne dai Bosco Ntaganda a wani mataki da ba a taba ganin irin sa ba ya mika kansa ga ofishin jakadancin Amurka da ke Kigali inda ya bukaci da a mika shi ga kotun da ke hukunta laifukan na yaki da ke birnin Hague na kasar Holland domin yi masa shari'a.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadisou Madobi