1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake taron taimakawa Libanon a birnin Paris

January 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuTP
A birnin Paris na kasar Faransa, wakilai daga kasashe kimanin 40 da kuma kungiyoyi da dama na kasa da kasa a yau zasu gudanar da taron masu tara kudin taimakon sake gina kasar Libanon bayan yakin da aka gwabza tsakanin kungiyar Hisbollah da Isra´ila. FM Libanon dake shan matsin lamba daga masu goyon bayan Syria, Fuad Siniora ya na halartar taron na birnin Paris. Sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice ta sanar da cewa Amirka zata ba wa Libanon taimakon kudi dala miliyan 770, yayin da Faransa mai masaukin baki zata ba da Euro miliyan 500 sannan KTT zata ba da euro miliyan 400.