A yau ake kammala taron kungiyar Commonwealth a Malta | Labarai | DW | 27.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake kammala taron kungiyar Commonwealth a Malta

Shugabannin kasashen kungiyar Commomwealth dake kammala taron kolin su a yau lahadi a Malta, sun yi kira ga KTT da ta yi sassauci akan tsarin ta na tallafawa aikin noma, wanda kasashe matalauta suka ce ba bu adalci a ciki. A cikin wata sanarwa da suka bayar kasashen na Commonwealth sun ce kudaden kwasta da kungiyar EU ke dorawa kayan amfani gona da ake shiga da su cikin kasashen ta na kawo cikas ga kokarin da kasashe masu tasowa ke yi na sayar da kayakin su a kan farashin da ya dace a kasuwannin Turai. A lokaci daya kuma shugabannin sun lashi takobin kara himmatuwa don cimma wata yarjejeniyar ciniki ta duniya wadda zata taimakawa kasashe matalauta. Sanarwar akan harkokin cinikaiyar ta bayyana damuwar da Commonwealth din ke nunawa ko shin kwalliya zata biya kudin sabulu a taron kolin kungiyar cinikaiya ta duniya da za´a yi a Hongkong a cikin watan desamba.