1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau aka cika shekaru 2 da hare-haren ta´addanci a London

July 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuGo

A yau Birtaniya ta yi bukin cika shekaru biyu da kai hare haren bama-bamai akan tsarin sufurin birnin London. FM Birtaniya Gordon Brown da ministocin gwamnati sun ajiye furanni a tashar jirgin karkashin kasa ta King´s Cross don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a hare hare. A ranar 7 ga watan 7 na shekara ta 2005 wasu ´yan kunar bakin wake su 4 suka kai hari a cikin jiragen karkashin kasa 3 da wata bas, inda suka halaka kan su da kuma mutane 52.