A Najeriya kotu ta soke zaben sanata Buruji Kashamu | Labarai | DW | 09.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Najeriya kotu ta soke zaben sanata Buruji Kashamu

Kotun birnin Abeokuta ta soke zaben sanata daga jihar Ogun a sakamakon kura-kurai da ta ce an tabka cikin rumfunan zabe kimanin dari a lokacin zaben.

A wannan Juma'a ce wata kotun birnin Abeokuta da ke a kudu maso yammacin kasar ta soke zaben sanata Buruji Kashamu wanda kasar Amirka ke nema ruwa a jallo domin kamashi a bisa zargin safarar hodar ibilis.

Sai dai kotun ta ce ba a bisa wannan dalili ba ne ta soke zaben nasa. Ta yi haka ne a bisa dalilin tarin kura-kurai da ta ke zargin an aikata a runfunan zabe kimanin 100 a lokacin zaben da ya gudana.

A watan Mayun da ya gabata ne dai kotu ta bada umarnin tsare Kashamu wanda aka zaba a watan Mars a matsayin sanata da ke wakiltar jihar Ogun a gidansa a wani mataki na shirin mika shi ga hukumomin kasar Amirkar kafin daga bisani wata kotun birnin Lagos ta bada umarnin dakatar da matakin shirin mika shi din.

Yanzu dai alkalin kotun birnin na Abeokuta Tobi Ebimowei ya ce za a sake gudanar da zaben a runfunan zaben da matsalar ta shafa.