A Najeriya harkokin jiragen sama na fuskantar matsala | Siyasa | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A Najeriya harkokin jiragen sama na fuskantar matsala

A Najeriya sashin harkokin jiragen saman kasar na kara shiga mawuyacin hali saboda tsada da karancin man jirgin da ma koma bayan tattalin arziki da sashin ke fuskanta.

Daya bayan daya dai kamfanonin sufurin jiragen sama na dakatar da aiyyukansu na jigilar fasinjoji a kasar, an dai fara ne da kamfanonin First Nation da Aero yanzu kuma ga na Arik ya bi sahu dukka a yanayi da ke nuna halin da wannan muhimmin sashi na sufurin jiragen sama ke ciki.

Karancin man jirgin na daga cikin dalilan da ya sa wasu kamfanonin suka rufe

Karanci da ma tsadar man jiragen sama ya tilasta wa kamfanonin jiragen sama da dama musamman na kasashen waje zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar irin na Ghana domin su sha mai kafin gudanar da harkokinsu. Tuni dai masu amfani da jiragen da kan samu kansu a tsaka mai wuya ke koken halin da ake ciki na rashin tabbas, musamman karuwar farashin tikitin shiga jiragen a cikin gida da a yanzu ya zama sahihiyar hanya ta tafiya saboda yawaitar matsalar ‘yan fashi da masu garkuwa da jama’a a kan hanya.

Kokari da gwamnatin ta Najeriya ke yi domin inganta lamarin

Nigeria Flughafen Katsina

Duk da ci gaban da ake ganin an samu a wannan sashi na raguwar afkuwar hatsurran jiragen sama, ci gaban na neman zama irin na mai ginar rijiya, abin da kwararru ke bayyana illarsa. Kokarin neman mafita daga wannan lamari da ya samu sashin sufurin jiragen saman Najeriya muhimmin mataki ne. Amma ga Injiniya Ahmed Idris masani a kan harkokin filayen jiragen sama na mai bayyana cewar sai fa an sake lalle.

''Sashin sufurin jiragen saman Najeriyar dai ya dade yana fuskantar kalubale iri daban –daban a tarihin kafuwarsa, kama daga yawaitar hatsura ya zuwa na rashin kayan aiki na zamani baya ga rashin igantattun jirage.''

Sauti da bidiyo akan labarin