Ɗan ƙunar baƙin wake a Pakistany a kashe mutane shida | Labarai | DW | 09.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɗan ƙunar baƙin wake a Pakistany a kashe mutane shida

Rundunar sojin Pakistan ta ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ya halaka mutane shida lokacin da ya kai harin bam kan wani wurin bincike na ´yan sanda dake arewa maso yammacin kasar. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai yara biyu da dan sanda daya, inji wani kakakin sojin kasar. Harin da aka kai a yankin na Swat ya zo ne kwana guda daya bayan da sojojin suka yi iƙirarin cewa sun fatattakin kusan dukkan masu tsattsauran ra´ayi daga yankin. An dai shafe makonni ana dauki ba dadi tsakanin sojoji da magoya bayan wani malami mai tsattsauran ra´ayi a yankin na Swat.