Ƙasashen EU na matsa kaimi a yarjejeniyar Ukraine | Labarai | DW | 17.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen EU na matsa kaimi a yarjejeniyar Ukraine

Yarjejeniyar da aka Ƙulla tsakanin Ukraine da Rasha na ci gaba da fiskantar matsaloli gabanin fara hunturun sanyi a Ƙasashen turai.

A wani Ƙokari na ganin an Ƙulla ingantacciyar yarjejeniyar diflomasiya manyan shugabannin Ƙasashen Turai sun gana da shugaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha da takwaransa na ƙasar Ukraine Petro Poroshenko a ranar Jumma'a nan , inda aka ɗan samu ci gaba sa dai ba a kai ga kai wa ga mafita ba ga rikicin Ukraine.

Shugaba Putin da Poroshenko sun gana a ranar Jummaar nan tare da manyan jami'ai daga Ƙungiyar ta EU da shugabannin Jamus da Faransa da Italiya da Birtaniyaa wani ɓangare na babban taron ƙasashen Turai da Asiya a Milan.