1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaba Erdogan zai ziyarci Jamus

November 11, 2023

A karon farkon cikin shekaru uku Shugaba Erdogan na Turkiyya zai ziyarci kasar Jamus a daidai lokacin da kasarsa ke takun saka da takwarorinta na kungiyar NATO.

https://p.dw.com/p/4Ygys
Shugaba Erdogan zai kawo ziyara Jamus
Shugaba Erdogan zai kawo ziyara JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A yayin wannan ziyara da ke zama ta farko da Recep Tayyip Erdogan zai kawo Jamus cikin shekaru uku, shugaban zai gana da shugaban gwamnatin Olaf Scholz a ranar Juma'a mai zuwa kamar yadda kakakin gwamnatin ta  Berlin ta tabbatar.

Karin bayani:  Erdogan ya soki sabon rikicin Gabas ta Tsakiya

Wannan ziyara dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Turkiyya da membobin NATO a game da rikicin Isra'ila da Hamas wanda ya barke kwanaki 35 da suka gabata.

Tattaunawar shugabannin biyu za ta mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda kakakin gwamnatin Jamus ta shaida wa manema labarai.

Karin bayani:  Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra'ila, tare da yanke duk wata hulda da Firminista Benjamin Netanyahu

A baya dai mista Erdogan ya kakkausar suka ga Isra'ila tare da zarginta da aikata laifukan cin zarafin bil adama a zirin Gaza inda ya kirayi jakadan Turkiyya daga kasar don nuna bacin ransa.