1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Turkiyya na son Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza

November 6, 2023

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bukaci sakataren harkokin wajen Amurka da ya dauki mataki cikin gaggawa na tsagaita bude wuta a zirin Gaza wanda dakarun Isra'ila ke ci gaba da yi wa ruwan bama-bamai.

https://p.dw.com/p/4YSm7
Turkiyya ta bukaci Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza
Turkiyya ta bukaci Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a GazaHoto: Jonathan Ernst/AP Photo/picture alliance

A yayin ganawar da jami'an biyu suka yi a ranar Litinin (06.11.2023), Mista Hakan Fidan ya jaddada wa takwaransa na Amurka Antony Blinken cewar ya zama wajibi a dakatar da Isra'ila kan hare-haren da ta kai wa kan mai uwa da wabi a Gaza, sannan kuma ya kamata a tsagaita wuta take yanke.

Karin bayani:  Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce adadin Falasdinawan da hare-haren Isra'ila suka hallaka ya haura dubu tara

To sai dai daga nasa bangare mista Blinken ya ce a baya-bayan nan an samu babban ci gaba a game da shigar da karin kayan agaji zirin na Gaza, sannan kuma Washington ta bukaci Isra'ilar da ta takaita hare-haren da ta kai wa wadanda ke janyo asarar rayukan fararen hula.

Karin bayani: Kungiyoyin agaji na kiran da a kawo karshen luguden wuta a Zirin Gaza

A baya dai Amurka da ke zama abokiyar huldar Isra'ila ta farko a ta fuskar siyasa da kuma soja ta nuna adawa ga matakin tsagaita bude wuta a Gaza sai dai amma ta goyi da bayan dakatar da hare-hare na dan lokaci domin ba da damar isar da kayan agaji da suka makale a iyakar Masar i zuwa zirin.