1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra'ila

November 4, 2023

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya dora alhakin mutuwar farafen hular Zirin na Gaza a kan Firministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

https://p.dw.com/p/4YPL7
Hoto: DHA

Turkiya ta ce za ta janye jakadanta da ke Isra'ila, tare da yanke duk wata hula da Firministan kasar Benjamin Netanyahu, a wani mataki na nuna bacin ranta a kan  zubar da jinin da ke faruwa a Zirin Gaza.

Karin bayanMajalisar Dinkin Duniya ta fara tattara hujjojin zargin aikata laifukan yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Gazai:

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ce ta sanar da hakan yau Asabar a Ankara babban birnin kasar, inda ta ce ta kira jakadanta a Isra'ila Sakir Ozkan Torunlar domin dawowa gida, inda za ta yi nazari kan halin zubar da jinin da ke faruwa yanzu haka a Gaza, sakamakon barin wutar da Isra'ila ke ci gaba da yi babu kakkautawa a kan fararen hula, tare da kin amincewa da tsagaita wuta.

Karin bayani:Daruruwan baki sun fice daga Gaza

Matakin Turkiyyar wadda ta fito fili karara ta nuna goyon bayanta ga Falasdinawa, na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke shirin kai ziyara Turkiyya.

Tun da farko dai shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya dora alhakin mutuwar farafen hular Zirin na Gaza a kan Firministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.