1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

MDD ta fara tattara hujjojin yakin Isra'ila da Hamas a Gaza

November 3, 2023

Firministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shaidawa Amurka cewa babu batun tsagaita wuta da zai amince da shi game da yakin Gaza, har sai Hamas ta sako Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su

https://p.dw.com/p/4YOG0
Hoto: Israel Defense Forces via AP/ Photo/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana tattara bayanai da kuma hujjojin zargin aikata laifukan yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, tun bayan barkewar rikicin a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu tara da dari biyu, da kuma Isra'ilawa dubu daya da dari hudu.

Rikicin dai ya tilastawa dubban Falasdinawa tserewa daga Zirin Gaza don tsira da rayukansu.

Firministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shaidawa Amurka cewa babu wani batun tsagaita wuta da kasarsa za ta amince da shi game da yakin Gaza, har sai kungiyar Hamas ta sako Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su baki-daya.

Mr Netanyahu ya bayyana hakan a juma'ar nan bayan kammala ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, bayan wata ziyara da Mr Blinken ya kai Isra'ila.

Isra'ila ta ce yanzu haka dai 'yan kasarta 249 ke tsare a hannun mayakan Hamas a Gaza, yayin da Mr Blinken din ya jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ilar ta ko wane hali.

Gidan Talabijin na Al-Aqsa ya rawaito ministan lafiyar Gaza na cewa wani harin sojojin Isra'ila a juma'ar nan kan tawagar motocin asibiti da ke dauke da marasa lafiya ya hallaka Falasdinawa da dama a Gaza.