1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Asibitoci da dama sun rufe a Zirin Gaza

November 2, 2023

Akalla asibitoci 16 daga cikin 35 a Zirin Gaza sun dakatar da ayyukansu saboda karancin makamashi musamman mayukan da suke sanyawa a injunan bayar da hasken wutar lantarki.

https://p.dw.com/p/4YKDa

Ma'aikatar lafiya a yankin Falasdinu da ta fitar da wannan labari a wannan Alhamis, ta ce wasu asibitocin da suka saura suna aikin ba su iya bayar da gamsasshiyar kulawa ga marasa lafiya.

Matakin Isra'ila na toshe hanyoyin shigar da makamashin mai da wutar lantarki gami da ruwan sha, ya jefa rayuwar mazauna Gaza cikin garari.

Dubban fararen hula ne dai ke fakewa aasibitoci tun bayan kaddamar da hare-haren ramuwar gayya da IsIsra'ilar ta yi, bayan harin ranar bakwai ga watan jiya da kungiyar Hamas ta yi, wanda ya yi jallin mutane sama da dubu da 400 a Isra'ila.

Rahotannin da ke fitowa daga Zirin na Gaza dai na cewa dakarun Isra'ila na dannawa ta kasa, daidai lokacin da adadin falasdinawa da suka rasa rayukansu a yakin ya zarta mutum dubu tara a yanzu.