1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

WHO ta bukaci daina kai hari asibitoci

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci a daina kai hare-hare a duk wasu cibiyoyin kiwon lafiya, kwana guda bayan mummunan hari da aka kai a wani asibiti a yankin Zirin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/4Xix1
Gaza | Hari | Asibiti | Rikici | Isra'ila | Hukumar Lafiya ta Duniya | Turai | Hans Kluge
Shugaban Hukumar Lafiya Duniya WHO, reshen nahiyar Turai Hans KlugeHoto: DW

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO reshen nahiyar Turai Hans Kluge ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce suna kira da a yi duk mai yiwuwa wajen dakile kai hari a cibiyoyin kiwon lafiya. A cewarsa wannan kiran shi ne babban abin da suka sanya a gaba, kana abu na biyu shi ne tabbatar da kare rayukan fararen hula ta kowacce hanya.