1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

NATO: Yakin Ukraine zai dauki lokaci

September 17, 2023

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO ya yi gargadin cewa a fidda tsammanin kawo karshen yakin Ukraine cikin gaggawa, sannan ya bukaci kasashe mambobin kawancen da su kara shiri.

https://p.dw.com/p/4WRaC
Ukraine | NATO | Jens Stoltenberg
Shugaban kungiyar Tsaro ta NATO Jens StoltenbergHoto: PETRAS MALUKAS/AFP

Jens Stoltenberg ya yi wannan furici ne a wata hira da ya yi da kamfanin yada labarai na kasar Jamus da ake kira Funke, inda ya ce a mafi yawan lokuta yaki na dadewa fiye da lokacin da ake tsammani, don haka ya zama wajibi kasashen kungiyar su shirya damarar yin dogon yaki a Ukraine. To sai Stoltenbergya ce kawancen na NATO na son zaman lafiya, to amma abin la'akari shi ne idan Shugaba Volodymyr Zalensky da 'yan Ukraine suka ajiye makamai to kasarsu za ta shafe daga doron duniya. Wannan gargadi na sakataren kungiyar ta NATO na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Kiev ke ci gaba da kai farmaki domin fatattakar takwarorinsu na Rasha daga yankunan Ukraine da suka mamaye.