1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Olaf Scholz ya gana da Xi Jinping na Chaina kan Gaza

November 3, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gana da shugaba Xi Jinping na Chaina kan Gaza

https://p.dw.com/p/4YNQO
Hoto: Kay Nietfeld /AFP

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gana da shugaba Xi Jinping na Chaina ta bidiyo yau juma'a, inda suka tattauna kan batun rikicin Gaza da kuma halin da yankin ke ciki a yanzu, da kuma yadda za su samu hadin kai da juna ta fannin harkokin tattalin arziki.

Karin bayani:Dangantakar Jamus da China mai sarkakiya

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magan da yawun gwamnatin Jamus ya fitar yau, yana mai karin bayanin cewa shugabannin biyu sun kuma tattauna kan yakin Rasha da Ukraine da ya shafe watanni 20 ana gwabzawa.