1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Makamanciyar kyautar Nobel 2023

September 29, 2023

An karrama wasu mata biyu ‘yan kasashen Afirka saboda ayyukan da suke gudanar na taimakon rayuwar al'umma da makamanciyar kyautar Nobel. Matan ‘yan fafutuka sun fito ne daga Ghana da kuma Kenya

https://p.dw.com/p/4WyvK
Phyllis Omido mai fafutukar kare muhalli
Phyllis Omido mai fafutukar kare muhalliHoto: Goldman Environmental Prize

Da farko dai wannan kyauta ce da aka bai wa Phyllis Omido ‘yar asalin kasar Kenya da ma wata kungiya mai rajin kare muhalli tare da kai dauki domin ceto bakin haure a tekun Bahar Rum mai asali daga Cambodia. Sai kuma wata 'yan kasar Ghana Eunice Brookman-Amissah.

Matan masu fafautuka sun samu kyautar ce da ake kira Alternative Nobel, makamanciyar kyautar Nobel da wani mai taimakon jama'a Bajamushe da ke da dangantaka da Sweden, Jakob von Uexkull ya kirkiro a shekara ta 1980.

Wadanda suka ci kyautar dai za su raba wasu makudan kudade a tsakaninsu wadanda ba a bayyana adadinsu ba saboda dalilai na tsaro, ganin irin taimakon da suke bai wa al'uma ta fuskoki da dama.

Ita dai Phyllis Omido 'yar asalin kasar Kenya, wadda ake kiranta Mama Moshi wato uwar hayaki, ta yi fice ne a gwagwarmayar kare yanayin muhalli a yankunan da take rayuwa a cikinsu a yankin Mombasa na Kenya.

Phyllis Omido 'yar kasar Kenya mai fafutukar kare muhalli
Phyllis Omido 'yar kasar Kenya mai fafutukar kare muhalliHoto: Imago Images/Zuma/J. Wakibia

Karin Bayani: Illar sauyin yanayi a Afirka

Ta kama wannan fafutuka ne dai bayan aiki da ta yi a wani kamfanin da ke narkar da sinadaran hada batura da ke a Owino Uhuru, a wajen birnin Mombasa. Aikin da ake yi a wajen ya taba lafiyarta da ta wani danta da ma sauran wasu mutane masu yawa a kauyen, abin kuma da ya zaburar da ita wajen kare muhalli.

Omido na cewa "Abu mafi muni shi ne bayan aikin wata daya kacal da na yi a wannan kamfani, dana ya kamu da rashin lafiya, an kuma yi masa gwajin cututtukan da aka sani duk, babu su a tare da shi. Sai wata kawata ta zo da wata shawarar cewa a yi masa gwajin guba mana, na tambaye ta dalili sai ce min ai inda kike aikin nan, akwai guba mai hadari.

Daga cikin ayyukan Eunice Brookman-Amissah ‘yar asalin Ghana kuwa, sun taimaka wajen samar da dokar kare rayuwar mata a bangaren zubar da ciki a kasashen Ghana da Zambia da Malawi. Ta fito fili a fafutukar da ta yi na bai wa mata ‘yancin zubar da ciki a shekarun 1990, abin da ake gani kafin lokacin wani abu ne mai muni ko ma abin kyama.

Eunice Brookman-Amissah 'yar Ghana da ta sami makamanciyar kyautar Nobel
Eunice Brookman-Amissah 'yar Ghana da ta sami makamanciyar kyautar NobelHoto: Agyemam-Duah

Eunice Brookman-Amissah ta ce a lokacin da muka fara wannan gwagwarmayar, furta kalmar zubar da ciki kadai haramun ce, ba ka ma isa ka yi ta a cikin mutane ba. Amma haka muka yi tsaye sai da muka kai ga nasara. Wannan sam ba abu ne da aka yarda da shi ba, ganin cewa ba macen da ya kamata ta rasa ranta a kan wani abu da a likitance ake iya magantawa, musamman zubar da ciki da kwararru ke yi da kansu.

Kasashen Afirka bakar fata dai na daga cikin kasashen duniya da ke cikin hadari kwarai da gaske a fannin mace-macen matan da ke daukar juna biyu da suke nadamar samu.

Ana dai samun matan da kan zubar da ciki mai hadari sama da miliyan shida da dubu dari biyu a kowace shekara, inda ake ganin aikin Eunice Brookman-Amissah da ya kankama cikin farkon shekarun 2000 ya rage adadin da kashi 40 cikin dari musamman na matan da ke mutuwa saboda rashin damar zuwa wajen likita ba tare da wata matsala ko kyama ba.