1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP26: Musayar yawu a kan sauyin yanayi

November 4, 2021

Shugabannin kasashen duniya sun himmatu a kan batun sauyin yanayi a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a kan muhalli da aka fara a ranar Lahadi a birnin Glasgow.

https://p.dw.com/p/42Zpq
Glasgow, Schottland | COP 26 UN-Klimakonferenz | US Präsident Joe Biden
Hoto: Erin Schaff/AP/picture alliance

A makon da ya gabata ne birnin Glasgow na Scotland a Birtaniya, ya karbi bakwancin kasashen duniya akalla 200 da suka soma taron koli na Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi wato COP26, da zummar ci gaba da tattauna yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris. Manufar babban taron ita ce na rage hayaki mai haddasa dimamar yanayi da duniya ke fuskanta zuwa kasa da digo biyu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa duniya na cikin wata mummunar barazana ta dimamar yanayi da ya zarta maki biyu da digo bakwai, lamarin da ya kai ta ga cewar dole sai an zage damntse. Ko baya ga Majalisar Dinkin Duniya kwararru kan yanayi da kungiyoyin rajin kare muhalli, sun yi ittifakin cewa matakan da duniya ke dauka a yanzu kan hayaki mai gurbata muhalli basu taka kara suka karya ba.