1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan gudun hijira sun mutu a teku

September 29, 2023

Dubban mutane ne suka yi kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai daga kasashen Afirka kudu da hamada. Kaso mai yawa daga cikin su ne dai suka mutu a wannan shekara.

https://p.dw.com/p/4WwaL
Aikin ceto a tekun Bahar Rum
Aikin ceto a tekun Bahar RumHoto: Pau de la Calle/AP/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 2,500 ne suka salawanta a tekun Bahar Rum kadai a wannan shekarar, a yayin da suke kokarin shiga kasashen Turai ba bisa ka'ida ba.

Hukumar kula da agaji ta majalisar duniyar UNHCR, wadda ta nuna damuwa, ta kuma ce a bana bakin hauren da suka mutun sukaru sama da abin da aka gani a daidai wannan lokaci a bara. A baran dai mutum dubu da 680 ne aka yi kiyasin suka mutu a tekun.

Alkaluma dai sun nunar da cewa kimanin bakin haure dubu 186 ne suka shigo nahiyar Turai ta tekun a tsakanin watan Janairu zuwa 24 ga wannan wata na Satumba da muke ciki.

Daga cikin su akwai dubu 130 wadanda ke a Italiya a yanzu, saura dubu 500 kuma na kasashen Girka da Spain da Cyprus gami da tsibirin Malta.

Akasarin bakin na haure dai sun fito daga kasashen Afirka bakar fata.