1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka tana fuskantar illar sauyin yanayi

Usman Shehu Usman SB/ZMA
March 17, 2023

Jarirun Jamus sun duba yadda sauyin yanayi ke illa a Afirka da kuma yaduwar cutar amai da gudawa gami da shirin Jamus na horas da ma'aikata daga nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4Oq0N
Malawi | illar guguwa
Malawi illar guguwaHoto: Esa Alexander/REUTERS

Jaridar die Tageszeitung, wace ta duba batun kare mahalli, ta ce radadin illar sauyin yanayi na shafar kasashe, Jaridar dai na sharhi ne kann kasashen Malawi da Mozambik da Madagaska inda guguwar daka kira Freddy ta yi mummunar barna da ta shafi rasa rayuka masu yawa. Guguwar ta afku a kusan kilomita 1,500 a tsakiyar tekun Indiya, inda ta fara kadawa tun a tsakiyar watan Fabrairu. Masanan yanayi daga can nisan teku da ke ta bangaren arewa maso gabashin tsibirin Rodrigues a kasar Mauritius guguwar ta taso inda ta ratsa Madagaska da Mozambik a takaice har zuwa kasar Zimbabwe. Da farko guguwar ta dan lafa amma ta sake dawowa da garfin gaske kuma ta yi barna.

Malawi da Mosambik guguwa mai karfi
Malawi guguwa mai karfiHoto: NASA/AP Photo/picture alliance

Guguwar da aka yi wa lakabi Freddy tana da karfi hadi da tafiyan saurin kilomita 270 a cikin sa'a guda Wanda shi ne a kan kololuwarta a daya daga cikin guguwa mafi nauyi a tarihin Kudu maso Gabashin Afirka. A bisa alkaluman hukuma, an tabbatar da mutuwar mutane 263, kuma 225 daga ciki a Malawi.

Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung: labarin kiwon lafiya ta yi. Tana mai cewa Kwalara na yaduwa cikin sauri a kasashen Afirka da dama. A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), sama da mutane 130,000 ne aka gano da suka kamu da cutar a nahiyar Afirka tun daga bara zuwa yanzu. 

Afirka Mosambik cutar amai da gudawa
Ta'adin cutar amai da gudawa a MozambikHoto: Marcelino Mueia/DW

Haka kuma alkaluman suka ce sama da mutane 3,000 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalera. Yanayin karuwar da ake gani zai iya haifar da kamuwa da cutar kwalara fiye da na bariya, wanda ita ce shekara mafi muni a Afirka a cikin kusan shekaru goma a bisa masu illar cutar kwalera.

Kasar Jamus na son horar da ma'aikata a Afirka da kuma kawo su Jamus. Amma. Wannan shi ne sharhin jaridar Berliner Zeitung wace ta duba rahoton bukatar ma'aikata zuwa Jamus daga kasar Ghana.Jaridar ta ci gaba da cewa kasar Ghana da ke yammacin Afirka, wadda ke bakin teku masu zafin yashi, ba kasafai ake yin labarin kasar a shafin farko na jaridun Jamus ba. Sai dai kuma, a cikin 'yan kwanaki a karshen watan Fabrairu, Ghana ta kasance batun magana a kafafen yada labaran Jamus, lokacin da ministan kwadago Hubertus Heil da ministar raya kasashe Svenja Schulze suka ziyarci kasashen Ghana da Cote d'Ivoire, kan batun duba mutanen da ke samun horon sanin makamar aiki da ake shirin kawo su kasar Jamus, cikin sabon shirin gwamnatin Berlin na nemo ma'aikata daga kasashen waje.

Najeriya | Kayan tahirin masarautar Benin da aka dawo da su birnin Abuja
Kayan tahirin masarautar Benin a NajeriyaHoto: Florian Gaertner/photothek/IMAGO

Jaridar Die Welt sharhinta shi ne kann batun kayan tarihin masarautar Benin a Najeriya da turawan mulkin malllaka suka sace. Tana mai cewa mene ne makomar tagulla? Bayan dawo da kayan tarihin Benin na farko daga Jamus, har yanzu ba a baje kolin su a Najeriya ba. Hasali ma a yanzu dai wani taro ya bayyana sabani tsakanin masu wadannan kayan tarihi, kusan watanni uku kenan da kasar Jamus ta mikawa Najeriya tagulla guda 22 na Benin, a matsayin su ne kashi na farko daga daruruwan kayan tarihi da aka wawushe wanda yanzu Najeriya ke kokarin ganin an dawo mata da su.